1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

NATO na bukatar nazari kafin karin sojoji a Afghanistan

Yayin wani zaman taro da ta yi a birnin Tirana, kungiyar tsaro ta NATO ta bai wa kanta wata daya na yin nazari kafin ta bai wa Amirka amsa kan bukatar karin sojoji a Afghanistan.

Afghanistan Bundeswehr NATO Resolute Support Mission (picture-alliance/dpa/S. Mustafa)

Sojojin Jamus na kungiyar NATO a Afghanistan

Manyan hafsoshin sojojin kasashe 29 na kasashen kungiyar ne suka yi wani zama a birnin Tirana na kasar Albaniya, inda suka duba wannan bukata da Amirka ta gabatar musu. Shugabannin sojojin na kasashen kungiyar ta NATO sun amince cewa akwai bukatar karin sojojin a Afghanistan, amma kuma sai kowa ya sanar wa kasarsa irin bukatun kafin su sake zama a watan Oktoba mai zuwa domin ba da amsa ta karshe a cewar shugaban kwamitin sojojin na NATO Janar  Petr Pavel.

Taron dai ya samu halartar babban kwamandan sojojin kawancen da ke Afghanistan Janar John Nicholson, da kuma babban hafsan hafsoshin Amirka Janar Joe Dunford.

Ana ganin cewa Amirka na boye irin manufofin da take da su a kasar ta Afghanistan, inda take da sojoji tun daga shekara ta 2001. Amirkan dai ta ce tana bukatar karin sojoji a kasar ta Afghanistan wanda ake sa ran karin zai kai na soja 4000 a cewar wasu majiyoyi da dama. Yanzu haka dai akwai sojojin Amirka 11.000 a Afghanistan kaman yadda ma'aikatar tsaron kasar ta Amirka ta sanar wanda a baya ta bayar da adadin sojojin 8.400.