Nato na bukatar ayi gyara a Afghanistan | Labarai | DW | 22.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nato na bukatar ayi gyara a Afghanistan

Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta Nato, Jaap de Hoop yace dole ne ´ya´yan kungiyyar su kara kaimi, don samun nasarar da aka sa a gaba a Afghanistan.

Sakataren na Nato ya fadi hakan ne, a lokacin taron ministocin harkokin wajen ´ya´yan kungiyyar da aka gudanar a gefen taron Mdd da ake ci gaba dayi a birnin New york na Amurka.

A cewar Jaap de Hoop, kungiyyar ta Nato na bukatar ´ya´yan kungiyyar ne da cire wasu sarkafe sarkafen da suka makala ne, don bawa dakarun sojin dama na gudanar da aikin su yadda yakamata.

Don tabbatar da ganin an cimma wannan buri, sakataren na kungiyyar ta Nato ya kara jaddada muhimmancin aikin kungiyyar a kasar ta Afghanistan.....

Idan dai an iya tunawa, a makonni kadan da suka gabata, kwamandojin kungiyyar a Afghanistan suka bukaci karin soji don ci gaba da yakar yan kungiyyar Taliban dake ci gaba da kawo baraza a a kasar.