1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

NATO da kisan fararen hular Afghanistan

Dakarun NATO sun kashe fararen hula shida a Afghanistan bisa kuskure

default

Wasu fararen hula shida sun gamu da ajalinsu a Afghanistan biyowa bayan buɗe musu wuta da dakarun ƙungiyar tsaro ta NATO suka yi bisa kuskure. Wata sanarwa da rundunar ta wallafa, ta nunar da cewa wasu ƙarin mutane da ba ta bayyana yawansu ba, sun ji rauni a lokacin da sojojin na ISAF suka buɗe wuta a gundumar Paktia da ke kudancin Kabul. Wannan sanarwar ta biyo bayan tabbatarwa da rundunar ta NATO ta yi cewa, sojojinta na sama sun harbe wasu sojojin Afghanistan shida, shi ma bisa kuskure. Waɗannan kashe-kashen sun zo ne kwanaki ƙalilan bayan da Janar David Patraeus ya fara jagorantar rundunar da ta ƙunshi sojoji dubu 140. A wani labarin kuma sojojin Amirka biyar sun gamu da ajalinsu a fafatawa da masu tayar da ƙayar baya a Afghanistan.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Mohammad Nasiru Awal