1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Donald Trump ya haifar da mahawara

Salissou Boukari
November 10, 2016

Al'umma daga ko'ina na ci gaba da bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan zaben Donald Trump a matsayin sabon shugaban Amirka.

https://p.dw.com/p/2STKT
US-Präsidentschaftswahl 2016 - Sieg & Rede Donald Trump
Hoto: Getty Images/M. Wilson

Duk da cewar binciken jin ra'ayin jama'a da ma sauran masu lura da al'amuran siyasa sun bai wa 'yar takara Hillary Clinton nasara kafin zabe, amma 'yan kasar Amirka sun tabbatar da dan takara Donald Trump a matsayin sabon shugaban kasar Amirka wanda zai maye gurbin Shugaba Barack Obama.