1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nasarar kubutar da 'yan matan Dapchi

Zainab Mohammed Abubakar
March 22, 2018

Mahukuntan Abuja dai na kallon samo 'yan matan a matsayin babbar nasara ga shugaban kasar da ke fadin ya kusa kare yaki da ta’addanci amma kuma ya kalli satar mai tada hankali.

https://p.dw.com/p/2ulZh
Boko Haram lässt entführte Mädchen frei
Hoto: DW/A.S. Muhammad

 Duk da cewar dai sun taru da sunan taron mako mako, tsallen murna ya mamaye fuskoki da bakunan 'yan majalisar zartarwar Tarrayar Najeriyar da suka karbi labari na sakin 'yan matan a cikin farin ciki.

Wata tattaunawar da gwamnatin kasar ta ce ta kunshi kungiyoyi na waje da ma abokai na gwamnatince dai a fadar ministan harkoki n labarai na kasar ta yi sanadiyar sakin 'yan matan.


Tun a farkon makon ne dai dama aka ruwaito ministan tsaron kasar Janar Mansur Dan Ali mai ritaya yana baiyana yiwuwar saki na 'yan matan  da suka share tsawon wata guda a dokar daji suka kuma tilasta ziyara ta shugaban kasar ya zuwa kauyen Dapchin.