1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nasarar ganawa tsakanin kasashen Koriya

Suleiman Babayo MNA
January 9, 2018

Kwalliya ta biya kudin sabulu lokacin ganawa tsakanin Koriya ta Kudu da Koriya ta Arewa da ya gudana kan iyakar kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/2qXiN
Südkorea Gespräche zwischen Nord- und Südkorea in Panmunjom
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Yonhap/Korea Pool

Ganawa tsakanin Koriya ta Kudu da Koriya ta Arewa ta haifar da abin da ake bukata, inda mahukuntan Koriya ta Arewa suka amince da tura wakilai zuwa gasar guje-guje da tsalle-tsalle na Olympics na hunturu a watan Febrairu wanda ita Koriya ta Kudu za ta dauki nauyi. Wannan ke zama ganawa ta farko tsakanin bangarorin biyu tun shekara ta 2015 kimanin shekaru biyu ke nan.

Ministoci daga bangarorin biyu suka jagoranci wakilai zuwa wajen wannan tattaunawa, kuma ita Koriya ta Kudu ta nemi amfani da wannan dama domin dakile zaman zullumi a mashigin ruwan Koriya, sakamakon matakin Shugaba Kim Jong-Un na Koriya ta Arewa kan bunkasa makaman nukiliya.