Nasarar ceto a tarihin duniya | Labarai | DW | 13.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nasarar ceto a tarihin duniya

An kafa tarihi a ƙasar Chile bayan da mutumin farko ya fito doron duniya, bayan wata biyu cikin rami

default

Florencio Avalos, mutumin farko da aka ceto.

A ƙasar Chile an fito da mutumin farko daga 33 da suka maƙale cikin ramin haƙar ma'adinai tun watanni biyu da suka gabata. Florencio Avalos wanda ya fara fitowa ya samu tarba daga 'yan uwansa da ma shugaban ƙasar ta Chile kansa, harama da dubban 'yan jaradun da suka je ganin ƙoƙob. Masu ceton dai sun zura wata guga wanda ta kai har inda masu haƙar ma'adinan suke a ƙarƙashin mitia 622, inda ake saran za'a yi amfani da gugar wajen fiddo da dukkan mutanen. Mutanen sun kwace kwanaki 69 a ƙarƙashin ƙasa, kuma a tarin duniya babu wasu mahaƙa da ƙasa ta rubta kansu a irin wannan zurfin kuma suka fito da rai. Yanzu za'a ɗauki kwanaki biyu ana zaƙulo mutanen.

Mwallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu