1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NASA ta dage ranar harba kumbon Atlantis.

December 7, 2007
https://p.dw.com/p/CYaQ

Cibiyar binciken sararin samaniya ta Amurka, watau NASA, ta ɗage ranar harba kumbon Atlantis zuwa sararin samaniya, daga gobe asabar kamar yadda ada aka shirya, sabili da wasu matsaloli da suka shafi shirye-shiryen harba kumbon. Karo na biyu kenan NASA ke jinkirta shirinta na harba kumbon Atlatis cikin kwanaki biyu. Daman an shirya harba kumbon na Atlantis zuwa tashar binciken kimiya ta kasa da kasa dake cikin sararin samaniya, domin gudanar da bincike na tsawon kwanaki goma sha daya.