Nana Akufo Ado ya lashe zaben shugabancin kasa Ghana | Duka rahotanni | DW | 09.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Duka rahotanni

Nana Akufo Ado ya lashe zaben shugabancin kasa Ghana

Shugaban Ghana John Dramani Mahama ya amince da shan kaye a zaben shugabancin kasar har ma ya taya dan takarar adawa Nana Akufo-Ado murnar samun nasara.

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya amince da shan kaye a zaben shugabancin kasar da aka gudanar a ranar Laraba,.

John Mahama ya kira abokin hamaiyarsa ta wayar tarho kuma dan takarar jam'iyyar adawa NPP Nana Akufo Ado wanda ya lashe zaben yana mai taya shi murnar samun nasara

Tun da farko shugaba Mahama ya yi alkawarin martaba sakamakon zaben duk yadda ya kasance. 

Shugabar hukumar zaben Charlotte Osei ta sanar da sakamakon a hukumance inda ta baiyana Nana Akufo-Ado na jam'iyyar adawa ta NPP a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben shugabancin kasar ta Ghana. 

Ghana dai ita ce kasa mafi kwanciyar hankali a yammacin Afirka wadda dimokradiyyarta ta kafu.

Tuni magoya bayan sabon zababben shugaban Nana Akufo-Ado suka shiga shagulgulan murna da farin ciki.

Sauti da bidiyo akan labarin