Nan da wata daya za´a kafa gwamnatin wucin gadi a Nepal | Labarai | DW | 17.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nan da wata daya za´a kafa gwamnatin wucin gadi a Nepal

An shigar da ´yan tawaye masu ra´ayin Mawo cikin gwamnatin wucin gadi a kasar Nepal. Hakan dai ya zo ne bayan da gwamnati ta amince ta rusa majalsiar dokoki bayan wani taro na tarihi da aka yi tsakanin FM G.P. Koirala da shugabannin ´yan tawaye a birnin Kathmandu. Madugun ´yan tawaye Prachanda ya nunar da cewa nan da wata daya mai zuwa za´a kafa gwamnatin rikon. Ana ganin wannan sanarwa tamkar wata nasara ga masu ra´ayin Mawo wadanda suka dade suna neman a sake fasalta kundin tsarin mulkin kasar. A karshen watan afrilu kawancen jam´iyu 7 karkashin FM Koirala suka tilastawa sarki Gyanendra maido da majalisar dokoki kana kuma suka tube shi daga ikon sa. Bayan wannan lokaci gwamnati ta fara tattaunawa da ´yan tawaye.