1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nan bada jimawa ba za'a gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu---

Dantakarar neman shugabancin kasar Indonesia ya musanta cewar ya sami taimakon kudade daga waje---

default

Dankarar neman neman shuagbancin kasar Indonesia Sulsilo Bambang Yudhoyono ya mustan rade raden da ake yaadawa cewar shida jama’iyarsa sun sami taimako wajen gudanar da harkokin su daga kasahen waje.Tsohon janar din sojin kasar ta Indonesia Yudhoyono,da ya sami kashi 33.6 daga cikin dari na kuriun da aka kada a zaben shugaban kasar Indonsia da aka gudanar cikin watan Yulin da ya gabata na zaman daya daga cikin yan takarar neman kujerar shugabancin Indonesia da zasu kara da shugabar kasar mai ci a yanzu Megawati Sukarnoputri a zaben shugaban kasar da za’a gudanar zagaye na biyu ranar 20 ga wanan watan da muke ciki.

A bisa tsarin dokokin zaben Indonesia an bukatar dukan dan takarar neman shugabancin kasar,ya sami gagarumin rinjaye na kuriun da aka kada lokacin zabe,in ko ba haka ba sai tilas an sake gudanar da zabe zagaye na biyu.

Da yake jawabi ga manema labaru bayan da ya baiyana a gaban hukumar yaki da karbar rashawa ta kasar Indonesia,dan takarar neman shugabancin kasar kuma tsohon janar din soji Yudhoyono,y a fito fili ya musanta cewar shi da jama’iyarsa ta Democratic Party sun sami talafi na dola miliyan 50 daga Amurka wajen gudanar da kamfai dinsa na takarar neman shugabancin kasar Indonesia.

Yudhoyono ya nuna rashin jin dadinsa kann yadda aka rika raba wasu takardu dake dauke da bayanan dake nuna cewar kada ku zabi SBY saboda ya sami taimakon gudanar da kamfai dinsa na siyasa daga Amurka,don haka ne ma yace wanan zargi da ake yi masa bashi da tushe balantana makama.

Ya dai kara da cewar shi kam babu wani talafi na kudade da ya samu daga kasahen waje kamar dai yadda wasu ke yi masa wanan zargi.

Yudhoyono na zaman daya daga cikin jami’an sojin Indonesia da ya shafe shekaru yana karbar horon aiyukan soji a wata makarantar horar da sojin Amurka,nan din kuma ya sami baban degiri a harkar gudanarwa,wanda kuma dagantakarsa da jami’an diplomaciya na kasahen duniya a sabili da kwarewar da yake da ita a fanin magana da harshen turanci ya sanya ake zargin cewar ko shi dan korarn kasahen yammacin turai ne.

Rawar da Yudhoyono ya taka a matakan yaki da aiyukan tarzoma da kasar Indonesia ta bulo da shi,ya sanya an hukunta kungiyoyin tsagerun musulmin kasar masu yawa,kasancewarsa ministan tsaron shugaba Megawati,wanan dalilin ne ya sanya wasu ke zarginsa da cewar makiyin addinin Islama ne,a yayin da kashi 85 daga cikin dari na alumar kasar Indonesia dukanin su suka kasance musulmi.

Dan takarar neman shugabancin kasar ta Indonesia yace ya fata alumar Indonesia zasu jefa masa kuriun su lokacin zabe kuma su janye daga wanan zargi da suke yi masa,ya dai yi alkawarin magance matsaloli na rashin aikin yi,bunkasa ilimi da tattalin arziki matukar dai ya sami nasara darewa kann karagar mulkin Indonesia.

Baban kalubalen dake gaban dukan mutumin da sami nasarar hawa kujerar shugabancin kasar Indonesia a zaben da za’a gudanar zagaye na biyu shine,daukar matakan farfado da tattalin arzikin kasa,samar da aiyukan yi da kuma yaki da kungiyoyin tsagerun musulmin wanan kasa.

 • Kwanan wata 31.08.2004
 • Mawallafi Jamilu Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvgu
 • Kwanan wata 31.08.2004
 • Mawallafi Jamilu Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvgu