Najeriya:Za a kara bayyana barayin kasar | Siyasa | DW | 23.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya:Za a kara bayyana barayin kasar

Shaidu da dama sun ce a shirye suke su kara bayyana sunayen wadanda suka saci dukiyyar kasa a Najeriya ga hukumar EFCC.

Mahukuntan Najeriya sun ce suna samun tururuwar masu tsegumin kudaden sata a kasar bayan shirin tsegumi mai ladan da ke tashe cikin kasar a halin yanzu.Kama daga motocin alfarma ya zuwa ga makudai na kudade dai sannu a hankali Najeriyar na fuskantar sabon yanayi a cikin yakin hancin da a baya ya fuskanci turjiya.Ko a tsakiyar wannan mako dai gwamnatin kasar ta ayyana gano wasu tsabar kudade har Naira miliyan dubu takwas da dari hudu da aka boye a cikin wani asusun da babu mai shi a kasar.

Ko bayan nan kuma jami'an hukumar EFCC sun yi nasarar kwace wasu motocin alfarma a gidan tsohon shugaban hukumar fice da shigi har 17 a wani abin da ke zaman alamun sabon tsarin na aiki.Kwadayi na kudade a cikin halin kunci dai a fadar Dr Garba Umar kari da ke zaman wani mai sharhi kan hali na zamantakewar al'umma a kasar ya yi hasashen cewar karuwar masu tsegumta satar zai taimaka a samu barayin kasar da dama.

Sauti da bidiyo akan labarin