Najeriya:Fursunoni sun yi yunkurin tserewa
December 28, 2017Talla
Hukumar 'yan sandan jihar Akwa Ibom ta ce a yanzu sun cafke mutane bakwai da suka yi yunkurin tserewa daga gidan yari, amma ana ci gaba da farautar wasu fursunonin 36 da suka gudu.
Babu cikakkun bayanai kan adadin fursunoni da ke gidan yarin amma kungiyoyin kare hakkin bani Adam sun sha sukar hukumomin Najeriya kan rashin inganta rayuwar mutanen da ke kurkuku a fadin kasar.
Abinda wasu ke ganin baya rasa nasaba da abinda ke fusata fursunonin haddasa rigima da jami'an da ke tsaron kurkukun domin neman fita.