1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya za ta kara yawan sojoji a Zamfara

April 4, 2018

Gwamnatin Najeriya ta yanke shawarar jibge sojoji sannan kuma da cefane na makamai na kusan dalar Amirka miliyan dubu daya domin tunkarar kalubalen da ke fuskantar sassa na kasar.

https://p.dw.com/p/2vUtZ
Nigeria Maiduguri Militär Sicherheit Anti Boko Haram 2014
Hoto: picture-alliance/epa

A cikin watan Maris din da ya shude kadai dai sama da mutane 300 ne suka kai ga asara ta rayuwa sakamakon tashe tashen hankulan da ke dada kamari a sassan Arewa maso Yammacin Najeriya da kuma  ta gabas dama tsakiya da tai nisa a cikin rikici.

A can a sashen Arewa maso Gabashin Najeriyar dai an kai hari bisa fararen hula sau dai dai har 22 an kuma hallaka mutane 120 a cikin watanni uku na farkon shekarar da muke ciki. A yayin kuma da aka yi asarar rayuka kusan 60 a cikin makon jiya a garin Anka a wani hari na 'yan ina da kisa a jiha ta Zamfara.

Nigeria Wahlen 2011 Bild 1
Walwala kan yi karanci a gwamitsin soja da farar hula Hoto: DW/Gänsler

Karuwar ta'azzarar harin ne dai ya kai ga wani taron shugaban kasar da manyan hafsoshi na tsaro da nufin nazarin tashi na hankali da daga dukkan alamu ke neman rikidewa ya zuwa barazana mai girma.

Bayan kamalla taron dai ministan tsaron kasar Janar Mansur dan Ali mai ritaya ya ce Abujar ta yanke hukuncin turin sojoji da samar d kari na makamai da nufin tunkarar matsalar a kai tsaye. Ko  bayan yankin Ankan da ke da  asarar sama da mutane 60 a  wani harin da ya faru a karshen watan jiya dai, Abujar na kuma nazari na kari na matakai da nufin tabbatar da lafiya cikin tsakiyar Tarrayar Najeriyar.

Niger Niamey Angriff auf Gefängnis
Rasa rayuka a Najeriya bai tsaya ga farar hula baHoto: picture alliance/AP Photo

Tuni dai sojan kasar suka kara tsawon atisayen tseren beran da take a jihohin Nasarawa da Taraba da Benue dat sawon wasu watanni guda biyu bayan abun da ministan ya kira nasarar kwace makaman da sojan ke samu yanzu.Tarrayar Najeriyar dai na dada fuskantar zabe  a cikin yanayin rashin tsaron da ke neman tasiri ga batun zamantakewa da ma siyasa ta kasar.