Najeriya: Tsugune ba ta kare ba a kasafin 2016 | Siyasa | DW | 20.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Tsugune ba ta kare ba a kasafin 2016

Da alamu dai ta leko ta na shirin komawa ga fatan al'ummar tarayyar Najeriya na fara amfana daga kasafin kudin kasar da ke zaman irinsa na farko.

Präsident von Nigeria Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya

An dai share tsawon makonni sama da biyu ana zaman jiran tsamanni ga batun kasafin kudin kasar da ke zaman irinsa na farko ga sabuwar gwamnatin kasar. To sai dai kuma ana shirin kara jira a bangaren talakawa da ke fatan kasafin zai kai ga sauyi na rayuwa da ma rage radadi a bangare na 'yan kasar.

An kammala wani taron majalisar ministoci ta kasar tare da gwamnatin ta Abuja na cewar fa har yanzu da sauran aiki kan kasafin da ke fuskantar kace-nace cikin kasar.

Nigeria Kabinett Muhammadu Buhari Präsident

Zaman majalisar ministoci a Najeriya

Ministan kasafin kudin kasar Udoma Udo Udoma dai ya fada wa manema labarai cewar har yanzu ana tattaunawa kan kasafin a tsakanin fadar da kuma majalisun da ke kartar kasa ko mutuwa ko yin rai.

"A kan kasafin kudi na shekara ta 2016, har yanzu muna magana. A kan kasafi na shekara ta 2017 dai tunanin shi ne ya kamata a kai shi gaban majalisu a bana domin amincewa kansa ".

Ya zuwa yanzu wata tawaga ta mutane uku da suka hada da shi kansa shugaban kasar Muhammadu Buhari da mataimakinsa da ministan kasafin ne dai ke bin sidira bayan sidira suna nazarin kasafin da ake zargin an lullube shi da cika burin son rai a bangaren 'yan majalisar kasar ta Najeriya.

Sauti da bidiyo akan labarin