1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya tayi alkawarin shirya zabe na gari

October 3, 2014

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan, ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa zata shirya zabe na kwarai kuma mai inganci a shekara ta 2015.

https://p.dw.com/p/1DPBs
Hoto: picture-alliance/dpa

Shugaban yace, a shekara ta 2011 da ta gabata, sun samu yabo daga kashen duniya bisa yadda suka shirya zabe, kuma yana mai tabbatar cewa zaben 2015 zaiyi inganci fiye da wanda ya gabata. Shugaban ya sanar da wannan batu ne yayin da yake karbar sabin jakadun kasashen waje a kasar ta Najeriya, da suka hada da na kasar Spain,Ireland, Finland, da kuma na kasar Ghana.

Sai dai kuma wannan sanarwa, na zuwa ne a daidai lokaci da jagoran kungiyar Boko Haram wanda ake kira Abubakar Shekau ya sake bayyana ta wani sabon bidiyo, duk kuwa da cewa rundunar sojan Najeriya ta bada tabbacin mutuwar sa, kuma har ya sanar da girka shari'a a yankunan dake hannunsu. A kalla dai 'yan Boko Haram, na rike da garuruwa kusan 24 a cikin jihohi uku na arewa maso gabacin wannan kasa wanda ake ganin idan dai lamarin tsaron bai gyaru ba, to a kwai wuya Najeriya ta iya shirya zaben mai zuwa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu