Najeriya tana ci gaba da asarar fetur | BATUTUWA | DW | 13.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya tana ci gaba da asarar fetur

Majalisar wakilan Najeriya ta bayyana damuwa kan mumunar asarar da Najeriya ke ci gaba da tafkawa a sakamakon badakalar rijiyar mai ta Malabu da ake zargin sama da fadi.

Majalisar wakilan Najeriya ta bayyana damuwa kan mumunar asarar da Najeriya ke tafkawa sakamakon badakalar rijiyar mai ta Malabu da ake zargin sama da fadi na dala milyan 1.1 tun daga 1998 da har yanzu ba a kai ga warware matsalar ba balle hukunta wadanda ake zargi.

Badakalar ta rijiyar mai lamba 245 da aka fi sani da ta Malabu da tun daga 1998 ake takadama a kanta bisa zargin karkatar da kudin da ya kamata a bai wa gwamnatin Najeriyar a lokacin da aka yi cuwa-cuwar karbe rijiyar daga ainihin masu ita zuwa ga wasu fitattun ‘yan Najeriya da ake ci gaba da tafka shari’a a kanta.

Flüssiggasfabrik in Äquatorial-Guinea (Renate Krieger)

Yunkurin warware wannan batu na cin hanci da ke tattare da lamarin da ya sanya kwamitin majalisar wakilan gudanar da sauraren jin ra’ayin jama’a a kan badakalar rijiyar mai ta Malabu da ke da badakalakar mai ta sama da ganga bilyan tara don gane zahirin gaskiyar lamarin. Alhaji Lawal Abba shi ne ke wakiltar Mohammed Sani Abacha da su ne asalin masu kashi 50 na rijiyar ta Malabu ya bayyana abin da suke son ganin kwamitin ya yi.

"Waccan yarjejeniya da aka yi da ta saba dokokin Najeriya da na kasashen duniya wannan ikon a shugaban Najeriya ya soke sai a yi sabuwa don a mayar wa ainihin masu rijiyar man. Ta haka gwamnati za ta samu kudi kimanin dala bilyan bakwai kan wannan domin gyara ta’asar da aka yi.’’

Äquatorialguinea Energie Gasanlage in Malabo (AP)

Ma'aikatar shari’a da kamfanin mai na NNPC na cikin wadanda suka ba da ba’asi kan rijiyar man da bayanan suka nuna Najeriya na iya samun dala bilyan bakwai in har aka warware matsalar. Ko wane hali ake ciki a yanzu ga batun hukunta wadanda ake zargin sun yi rub da ciki da dukiyar gwamnatin Najeriya a kan batun? Mallam Abubakar Malami shi ne ministan shari’a na Najeriya.

‘’To babu halin da ake ciki a yanzu domin bincike ake yi, sai an kammala bincike sannan a san hali da matakin da za a dauka har yanzu muna kan bincike ne.’’

Amma ga kamfanin NNPC da su ma suka bayyana matsayinsu a kan wannan badakala da ke ci gaba da zama abin kunya ga Najeriyar.

Majalisar wakilan Najeriyar tana kokarin gano mai laifi ne domin hanzarta hukunta shi.

Sauti da bidiyo akan labarin