Najeriya: Tallafawa matasa da sana′ar hannu | Sauyi a Afirka | DW | 25.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Sauyi a Afirka

Najeriya: Tallafawa matasa da sana'ar hannu

A Najeriya Jefferson Omojuwa matashi ne da ya yi fice a fanin shafukan sada zumunta, amma a yanzu ya bullo da tsarin tallafawa matasa da kudadden da zasu iya fara sana’o'i, a matsayin hanyar talafa masu,

Tuni har wannan matashi ya taimakawa mutane 36 abinda ya jawo hankali wasu jama’a bada gudamawa a wannan harka da ba kasafai ake ganin haka ba a kasar. Ko me ya ja hankalinsa zuwa wannan da ma tasirin da hakan ke yi ga matsan da suka amafana? Daga Abuja Uwaisu Abubakar Idris ya aiko da wannan rahoton.


Jefferson Omojuwa matashi da ya yi fice a harkar shafukan sada zumunta a Najeriya, wanda in ka iske shi a ofishinsa tsaf-tsaf abinda zai fara zuwa ranka shine irin ‘yan kwalisar nan da suka taka tudun natsira da ba lasafai sukan waiwayi bay aba. Amma akasin haka ne, domin bias radin kansa ya samar da rabin miliyan na Nairar Najeriya, watau naira dubu 500 don talafawa matasa su damu fara kasuwanci ta yadda zasu dogara da kansu? Shin me ya dauki hankalinsa ne zuwa wannan.


Ya ce "kowa yasan kalubalen da ke fuskantar harakar kasuwanci a Najeriya, Najeriya na daya daga kasashen da ke da wahalar yin kasuwanci, kuma samun jarri abu ne mai matukar wahala, kudin ruwan da banki ke caji ya kai kashi 25 in ma ka samu bashin Kenan.  Ni duba cewa wasu dubu biyar ko goma kawai suke bukata, sai na ware Naira dubu 500 daga aljihuna nace bari in gwada in fara da ba mutane goma naira dubu 50 kowane in ga yadda zai kasance".


Wannan aiki da ya fara da rabin milyan ya ja hankalin wasu ‘yan Najeriya da suka bada tasu gudamawar abinda ya sanya aka samun Naira milyan 2.7 da aka talafawa matasa 36 da tuni wasunsu suka fara sa’aoi, ko wace hanya ya bi wajen zabensu sanin dama irin wannan zata iya sanya turuwar jama’a.