Najeriya ta shirya maye gurbin sojojinta da aka kashe a Darfur | Labarai | DW | 05.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya ta shirya maye gurbin sojojinta da aka kashe a Darfur

Gwamnatin Najeriya ta shirya sake tura sojojinta da zasu maye gurbin wadanda aka kashe karkashin dakarun AU a lardin Darfur.Babban hafsan tsaro a Najeriya Janar Andrew Owoye Azazi yace a ranar litinin zaa tura sojojin na Najeriya zuwa sansanin Haskanita domin fuskantar duk wani hari da zaa iya kai masu.Sojojin Najeriya 7 ne cikin 10 da yan tawaye suka kashe a ranar asabar data gabata a yammacin Sudan.

Shine kuma hari mafi muni da aka taba kaiwa kann dakarun AU tun lokacinda aka gike su a yankin a 2004.Yanzu haka dai kungiyar AU ta kaddamar da bincike kann wannan hari da aka kai.