Najeriya ta samar da sansani ga tubabbun ′yan Boko Haram | Labarai | DW | 06.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya ta samar da sansani ga tubabbun 'yan Boko Haram

Rundunar sojojin tarayyar Najeriya ta bayyana cewar ta samar da wani sansani domin kyautata dabi'ar tubabbun mayakan kungiyar Boko Haram.

Sanarwar ta ce sansanin wanda aka samar da shi zai yi kokarin ganin wadanda suka yi nadama da irin ayyukan da suka tafka sun shigo cikin al'umma ba tare da tsangwama ba.

To sai dai rundunar taki yin karin haske kan inda sansanin yake da kuma yadda za a gudanar da shi. 

Kazalika rundunar ta bukaci mayakan da su ajiye makaman su domin yin tuba in ba haka ba su kuka da kawunan su.

A kalla dai kimanin mutane dubu 20 rikicin Boko Haram yayi sanadiyar mutuwar su a yayin da sama da miliyan daya suka rasa muhallan su a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.