1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta mika wa Kamaru 'yan aware

Gazali Abdou Tasawa
January 30, 2018

Gwamnatin kasar Kamaru ta tabbatar da cewa Najeriya ta mika mata Sisiku Ayuk shugaban 'yan awaren yankin masu amfani da turancin Inglishi na kasar Kamaru wanda hukumomin Najeriyar suka kama a farkon watan Janeru. 

https://p.dw.com/p/2rk00
Kamerun | Unterstützer anglophoner Aktivisten aus Gefängnis entlassen
Hoto: Reuters/Stringer

Ministan harakokin sadarwa na kasar ta kamaru Issa Tchiroma Bakary ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa a jiy Litinin ne Najeriya ta mika wa Kamaru jagoran 'yan awaren da wasu magoya bayansa su 46 wadanda su dukkansu take tsare da su. 

Ministan Bakary ya bayyana cewa za a gurfanar da mutanen a gaban kuliya, kana ya kara da cewa kasashen biyu na Najeriya da Kamaru sun sha alwashin hada kai domin hana wa kungiyoyin 'yan ta'adda yin amfani da kasashensu wajen tayar da tarzoma ko tawaye a kowace daga cikin kasashen biyu.