Najeriya ta lashe gasar cin kofin Afirka na mata | Labarai | DW | 03.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya ta lashe gasar cin kofin Afirka na mata

Najeriya ta doke Kamaru a wasan karshe na cin kofin Afirka na mata wanda kasar ta Kamaru ta dauki nauyi.

Najeriya ta lashe gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka na mata, bayan doke kasar Kamaru da ci daya mai ban haushi. 'Yan wasan Najeriya sun samu nasarar jefa kwallon ana kusan tashi daga wasan.

Wasan wanda ya gudana a birnin Yawunde fadar gwamnati Kamaru, Najeriya ta zira kwallo a raga a mintoti 84, saura mintoci shida kadai a tashi a wasan, abin da ya jefa magoya bayan Kamaru kimanin 40,000 da ke cikin filin wasan cikin bakin-ciki.