Najeriya ta kama wani maaikacin Virgin Atlantic da hodar iblis | Labarai | DW | 09.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya ta kama wani maaikacin Virgin Atlantic da hodar iblis

Yan sanda a Najeriya sun dagatar da wani jirgin kanfanin Virgin atlantic daga tashi daga babban filin jirgin saman Lagos bayan kame wani maaikacin jirgin dauke da hotar iblis na cocaine da nauyinsa ya kai kilo 1.7.

Jamian yan sandan sunce jirgin yana shirin tashi ne zuwa birnin London a lokacinda jamian hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriyar.

Hukumar ta NDLEA ta bada wata sanarwar cewa maiakacin jirgin ya amsa laifinsa yana mai baiyana cewa wani dan Najeriya ne dake da zama a London ya bashi dala 4,000 domin ya kai wannan kunshi.

Najeriya tana daya daga cikin kasashe da suke yanke hukunci mafi sassauci ga masu sumogar miyagun kwayoyi a duniya.