1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta gano ma'aikatan boge dubu 50

Salissou Boukari
December 28, 2016

Fadar shugaban Najeriya ta sanar da kakkabe ma'aikatan boge har dubu 50, wanda hakan ya bai wa kasar damar yin tsumi na kusan miliyan 630 na Euro.

https://p.dw.com/p/2UwKJ
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: picture-alliance/AP Photo/C. Owen

Cikin wata sanarwa ce dai mai magana da yawun fadar shugaban kasar ta Najeriya Malam Garba Shehu ya tabbatar da hakan, inda ya ce kwatankwacin Naira miliyan dubu 200 da ake bai wa ma'aikatan na boge aka yi tsuminsu.

Sanarwar ta ce daga watan Fabrairu da ya gabata zuwa wannan wata na Disamba, an samu yin tsumi na Naira miliyan dubu 13 daga cikin albashin ma'aikata, yayin da binciken da aka aiwatar kan masu karbar kudaden ritaya, ya sa aka karbo wasu kudaden Naira miliyan dubu daya da miliyan daya a ko wane wata a tsakanin wannan lokaci a cewar Garba Shehu. Ya ce tuni aka mika mutane 11 daga cikin wadanda ke da hannu cikin lamarin a gaban hukumar da ke yaki da cin hanci ta EFCC.