Najeriya ta fara samun habakar tattalin arziki
May 10, 2017Tun a farkon fari dai hukumar lamuni ta duniya ta fitar da hasashen da ke fadin da akwai sauran tafiya a tsakanin Najeriya da kokari na ficewa a cikin halin masassara ta tattalin arziki. To sai dai kuma ta fara nuna alamun sauyi tare da wani sabon rahoton hukumar da ya ce tattalin arzikin na shirin kara ganin haske a shekarar badi. Tun daga zango na uku na shekarar bana dai a fadar rahoton na IMF da ya yi nazarin tattalin arzikin ya ce Najeriyar za ta kai ga ficewa a cikin halin koma baya na tattali arzikin da ta fada baya.
Ana dai kallon sauyi na tattalin arzikin na da ruwa da tsaki da zaman lafiyar da aka samu a Niger Delta da ya yi nasarar samar da yawan man kasar zuwa ganga miliyan biyu da doriya, a kullum tare da mayar da hankali ga harkar noma da ma'adinai cikin kasar.