1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Najeriya ta fara farfadowa daga koma-bayan arziki

February 15, 2017

Gwamnatin Najeriya ta nuna alamun kyautatuwar alkaluman tattalin arziki a daidai lokacin da talakawa ke kokawa kan tsadar rayuwa. Wasu daga cikin ‘yan kasauwa sun fara gani a kasa a ‘yan kwanankin da ake ciki. sai dai akwai bukatar gwamnatin ta ja damara don bunkasar ta dore.

https://p.dw.com/p/2XdAM

Bayan share tsawon lokaci cikin rudani, tarrayar Najeriya ta fara ganin alamun haske na ficewa a cikin massassarar tattali  na arziki, bayan share shekaru kusan biyu a cikin rukuki .Rahoton zango na Uku na tattalin arzikin ya tabbatar da karuwar da ta kai ta kaso .023 na tattali na arzikin, abin dake  nuna alamar karshen rikicin da ya dauki kasar a ba zata ya kuma jefata cikin halin ni 'yasu.

Gwamnatin Najeriya na fatan kawo karshen matsalar tare da da tabbatar da tasirinta a tsakanin 'yan kasar d ake zaman jiran tsammani na lokaci mai nisa. Abun kuma da ya sanya alamu na farfadowar ke zaman labari mai dadi ga gwamnatin da ke a tsakanin tasiri  a zukata na 'yan kasar da jefa kanta cikin kwandon tarihi na siyasar kasar.

To sai dai kuma  gwamnatin da ta dau 'yar lallashi da nufin shawo kai na tsagerun yankin Niger Delta mai arzikin man fetur. Abun kuma da  ya fara nuna alamar tasiri a cikin yawan mai dama farashinsa cikin kasar.