1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na son tallafin Ghana a fannin tsaro

Yusuf BalaSeptember 7, 2015

Shugaba Buhari na Najeriya ya bukaci tallafin takwaransa Mahama na kasar Ghana musamman ta fannin da ya shafi tattara bayanai na sirri a kan tsaro.

https://p.dw.com/p/1GSUI
Muhammadu Buhari steigt aus einem Flugzeug
Hoto: GettyImages/AFP/M. Safodien

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayyana bukatar tallafin takwaransa na kasar Ghana John Mahama wajen ganin sun tinkari kalubale da ke gaban kasar da suka hadar da batun tattalin arziki da matsalar tsaro.

Shugaba Buhari na wannan ziyara ta kwana daya a kasar ta Ghana ne cikin wani bangare na cikar wa'adin mulkinsa kwanaki dari a daidai kuma lokacin da kasar ta Najeriya ke fama da matsaloli na tsaro inda ya bayyana bukatar tallafin kasar ta Ghana musamman ta fannin da ya shafi tattara bayanai na sirri.

Ya ce "abu na farko mu sake saita alkiblar sojojinmu, mu saita su bisa tsari wajen bada horo da kara musu kayan aiki, da yadda za a rarrabasu wajen gudanar da aikinsu , ina ganin idan muna sauraron juna yadda ya kamata zai kyau ko kuma idan aka kalli yadda sojanmu suke za a ga mun takaita mayakan Boko Haram a wani kebattaccen wuri."