1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta bude shafin internet saboda Ebola.

September 4, 2014

Najeriya na bin sabbin dabarun ilimantarwa kan yaki da cutar Ebola ta hanyar intanet baya ga layin wayar hannu da aka bayar tun da fari dan tuntubar jami'an lafiya.

https://p.dw.com/p/1D7KX
Kampf gegen Ebola Symbolbild
Hoto: D.Faget/AFP/Getty Images

Wannan shafin da aka yi wa lakabin "Ebola Alert" bada bayanan Ebola, akwai kuma lambobin wayar tarho da aka bayar, inda likitoci ke jira ba dare ba rana. Kuma kamar yadda za a ji yadda cibiyar ke bada rahotanni, za a iya cewa a yanzu wannan lamarin ya sa mutane cikin dimuwa. Bodunrim Kehinde Paul ya bayyana irin wayoyin da suke samu kamar yadda ya bada misali.

"Wani mutum ya kiramu, yana gaya mana cewa akwai wata mace 'yar Laberiya dake siyar da abinci kusa da gidansu. Ta tafi gida Laberiya amma bata dawo ba. Ya yi wayanne domin 'yan sanda su tsare matar idan ta dawo tun daga filin jirgin sama. Domin kawai ita 'yar Laberiya ce, wai kada ta shigo da cutar Ebola. Wannan abun ban dariya ne"

Ko ba komai dai hakan ya bayyana yadda wasu 'yan Najeriya suka rude da labarin cutar ta Ebola, kazalika bude cibiyar ko-ta-kwana a birnin kamar Lagos za a iya cewa wani hobbasa ne ga hukumomin. Wadannan irin cibiyoyi da kuma wayoyin tarho za su kawar da bara-gurbi da ke yaudarar jama'a kamar yadda Lawan Bakare daya daga cikin wadanda suka kafa cibiyar ta ko ta kwana, ya yi karin haske.

Ebola in Lagos – Zwischen Panik und Normalität Pastor
Hoto: DW/A. Kriesch

"Akwai hatsari ga mutumin da yake ikirarin wai shi yana da riga kafin annobar cutar Ebola. Abin da zai iya kasancewa gare shi, shi ne wani mai dauke da cutar zai iya zuwa Cocin karban magani, kuma daga nan shi kansa ta yiwu ya kamu da cutar"

Wannan cibiyar ko ta kwana, likitocin sa kai ne suka kafa ta, inda kuma hakan ya bamu sambarka daga gwamnatin jihar Lagos, da kungiyoyin kiwon lafiya na duniya kamar WHO da UNICEF.

A cewar Lawan Bakare, sun samu nasar isar da bayanansu ga jama'a, inda ya bada misali a shafin sadarwa na Twitter kawai, an isar da kamfen dinsu ga mutane akalla miliyan biyu.

Ebola Seuche Afrika Helfer
Hoto: D.Faget /AFP/Getty Images

Yanzu haka dai a jihohi da dama na Najeriya an dauki matakan riga kafi, inda aka ware cibiyoyi na musamman, domin kula da masu fama cutar Ebola idan har ta bulla. Sai dai wasu lokutan irin matakan jami'an tsaro dama dimaucewar jama'a na wuce gona da iri, inda misali a wani otel dake Lagos 'yan sanda suka kama baki kimanin 39, wadanda ake zargin sun fito daga kasashen Saliyo da Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango, kasashen da aka samu bullar cutar ta Ebola.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yusuf Bala