1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta amince da matakan saisaita kasuwar mai

Zainab Mohammed AbubakarFebruary 23, 2016

Shugabannin Najeriya da na Saudi Arabiya sun marawa kokarin saisaita kasuwar mai baya, sai Najeriyar ta ki yin alkawarin rage yawan man da ta ke fitarwa ketare.

https://p.dw.com/p/1I0lG
Präsident von Nigeria Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Bayan tattaunawa a birnin Riyadh, shugaba Muhammadu Buhari da Sarki Salman sun lashi takobin daukar duk matakin da ya dace na dawar da martabar man petur a kasuwannin duniya, tare da daga farashinsa.

Ziyarar ta Buhari na zuwa ne mako guda, bayan taronkasashen Saudi Arabiya da Rasha da Venezuala da Qatar a birnin Doha, inda suka cimma yarjejeniyar cigaba da matakin da aka dauka a watan Janairu na rage yawan man da ake fitarwa ketare, idan har sauran kasashe masu arzikin man petur sun amince.

Sai dai yarjejeniya ta ta'allaka ne da amincewar manyan kasashe masu albarkatun man petur, kuma bisa dukkan alamu Najeriya za ta hade a wannan ayari.

Kamfanin dillancin labarun Saudiyya ya ruwaito cewar tattaunawa tsakanin mataimakin ministan mai na kasar Yarima Abdulaziz bin Salman da takwaransa na Najeriya karamin minista Emmanuel Ibe Kachiku, ya mayar da hankali ne kan hanya mafi dacewa na saisaita kasuwar man petur da hadin kai tsakanin kasashen da ke da mai domin cimma wannan manufa.

Daga Saudi Arabiyan, shugaban na Najeriya zai shige kasar Qatar.