1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sankarau ta kashe sama da mutane 700

Yusuf Bala Nayaya
April 19, 2017

A makon da ya gabata dai adadin mutane da aka bayyana da rasuwa ta sanadin cutar sun kasance 489 wanda mafi akasarinsu yara ne

https://p.dw.com/p/2bY7s
Symbolbild Forschungsbeziehungen Deutschland Afrika
Hoto: picture-alliance/Ton Koene

Cutar da ake zargin ta Sankarau ce ta hallaka mutane 745 a Najeriya, adadin da ke zama karin kimanin mutane 250 a sama da mako guda kamar yadda gwamnatin tarayya ta bayyana.

Sama da mutane 8,000 ne dai ake ganin sun harbu da kwayoyin cutar a fadin kasar kamar yadda aka samu rahotanni sama da watanni biyar. Kashi 93 cikin 100 na adadin sun fito daga jihohi biyar na Arewacin Najeriya. A makon da ya gabata dai adadin mutane da aka bayyana da rasuwa ta sanadin cutar sun kasance 489, mafi akasari yara abin da ya sanya shiga aikin rigakafin cutar ba kakkautawa. Jihohi biyar da annobar cutar ta Sankarau ta fi kamari dai na zama  Zamfara da Sokoto da  Katsina da Kebbi da Niger.