1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sabon tsari kan harkokin kiwo a Filato

Salissou Boukari
February 14, 2018

Gwamnatin jihar Filato ta ce ba za ta kafa dokar hana kiwo ba, amma za ta aiwatar da tsarin kebe dabbobi da ake kira "ranching" da ke a matsayin matakin samun zaman lafiya tsakanin makiyaya tare da manoma. 

https://p.dw.com/p/2sg1a
Frauen mit Ziegen in Zentral-Niger (Zinder)
Hoto: DW/Larwana Hami

Gwamnatin ta Filato dai ta ce tuni har ta kebe kudi naira milyan 250 cikin kasafin kudinta na bana wajen ganin wannan shiri ya sami nasara, kana ta ce kafin ta bullo da tsarin, ta kafa kommiti mai mutum 14, inda ya gana da shugabanin al'ummomi da shugabanin addinai da na matasa kan wannan kudiri. To sai dai a bangare guda, shugaban kungiyar matasan Berom na kasa Chiji Dalyop Chuwang, ya na gani yakamata gwamnati ta yi tuntumba sosai kafin ta aiwatar da wannan tsari na ta, don kuwa har yanzu akwai al'ummominsu da rikici ya sa suka gujewa kauyukansu, kada ayi amfani da wuraren su wajen bude wuraren kiwon.

Ra'ayi dai ya sha bambam kan wannan kudiri, domin acewar Alhaji Umar dan Shuwa Shettiman Bukuru, wanda ya dade yana saye da sayerwar dabbobi, bude wuraren kiwo ko ma labbin shanu abu ne da ke da matukar fa'ida a wannan hali da ake ciki. Sai dai kuma daga nashi bangare gwamnan jihar ta Filato Simon Lalong ya ce ya lura wasu 'yan siyasa na neman yin kafar ungulu ga wannan kudiri nashi ta hanyar yin amfani da matasa, don haka yake jan hankalin matasan jihar da su fahimci manufar sa. Abin jira a gani dai shine yadda wannan sabon tsari na kebe wuraren kiwo zai yi nasara ta yadda za'a kai ga samun bakin zaren warware duk wata takkadama ta tsakanin makiyaya da manoma a jihar Filato da ma kasa baki daya.