1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na zargin Amirka da yi mata leƙen asiri

November 7, 2013

Najeriya ta shiga sahun ƙasashen dake zargin Amirka da leƙen asirinsu, bisa bayanan da tsohon ma'aikacin leƙen asirin Amirka Edward Snowden

https://p.dw.com/p/1ADaa
Nigerian President Goodluck Jonathan speaks during a nationwide live broadcast on the state television on May 14, 2013. President Goodluck Jonathan has declared state of emergency in the nation's troubled northeast states of Yobe, Borno and Adamawa, where Islamic extremists now control some of the country's villages and towns, promising to send more troops to fight what is now an open rebellion. AFPPHOTO/PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Goodluck Jonathan President of NigeriaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Bayanan da suka nuna cewar Najeriya na cikin ƙasashen da hukumar tsaro da Amirka ke yi wa leƙen asiri ya haifar da damuwa a kan illar da wannan ke da shi ga yanayin tsaron Najeriya da a yanzu ya ke ciki wani hali na koma baya.

To an dai zargeta da naɗar bayanai na wayoyin tarho na shugabanin ƙasashen duniya da ma miliyoyin mutanen ba tare da izininsu ba, ya zuwa leƙen asirin hukumomi na tsaro da ci gaban ƙasa, abin da Amirka ba ta nuna wani gezau ko da na sani a kan hakan ba.

Bayanin da ya fito daga tonon sililin da ɗan ƙasar Amirkan nan Edward Snowden ke ci gaba da yi a game da zargin leƙen asirin da Amirkan ke yi da sannu a hankali ke bazuwa daga manyan ƙasashen da suke jin sun fi gaban Amirkan zuwa Najeriya, na ƙara bayyana yadda duniyar ke zama, wacce babu wani sirri a tsakanin ƙasashe.

An daɗe ana leƙen asiri

To sai dai ga Dr Aminu Abubakar, masanin kimiyyar aikewa da bayanai na zamani da kan shafi na sirri ya ce ba wai yanzu ne aka fara yin wannan leƙe-leƙe ba.

BILDAUSSCHNITT HANDOUT - Der Grünen-Politiker Hans-Christian Ströbele (r) überreicht bei seinem Besuch am 31.10.2013 in Moskau dem früheren US-Geheimdienstexperten Edward Snowden die Ehrenurkunde des Whistleblower-Preis 2013, welche ihm am 30.8.2013 die Organisationen IALANA, Transparency Deutschland e.V. und VDW (Vereinigung Deutscher Wissenschaftler e.V.) in Abwesenheit verliehen hatte. Foto: Irina Oho/dpa (Nur zur redaktionellen Verwendung bei Nennung der Quelle)
Edward SnowdenHoto: picture-alliance/dpa

"Ba wai Najeriya kaɗai ba, wannan leƙen asiri abu ne da tun asali da ma can ana yi, don haka zai yi wuya akwai wata ƙasa ta duniya da za ta ce ba'a yi mata leƙen asiri. In dai za ka ɗauki waya ka buga ma wani ko za ka hau kan na'ura mai aikin da kwakwalwa ta computer ka ce da aikawa wani sako to sai gyaran Allah, domin misalli ita internet ɗin nan ai Amirkawa ne suka yita, kuma ba wai sun yita ne domin ni da kai ba"

To sai dai tsoron illar da ke tattare da zargin leƙen asirin da Amirkan ke yi wa Najeriya ya shafi hukumar tsaro ta ƙasa ta SSS ta Najeriyar ne shi ne ya fi ƙara daga hankalin mutane da dama musamman sanin irin muhimmin rawar da hukumar ke da shi a batun tsaron Najeriyar, saboda ɗimbin bayanai na sirri da suke danƙare a hannun hukumar. Wannan ya sanya tambayar Malam Hassan Sardauna mai sharhi a kan al'amurran yau da kullum bayyana illar da ke tattare da hakan.

Leƙen asiri ɗabi'ar Amirka ne

"To idan har Amirka za ta iya leƙen asiri na jami'an hukuma ta tsaro ta farin kaya wacce ke da kima a idannun 'yan Najeriya ashe ka ga kowa ma kenan yana cikin hatsari musamman idan aka yi lakari da halin tsaro da ake ciki a Najeriya, domin kuwa idan har ƙasashe irin su Spaniya da Jamus suna kokawa kuma har ana naɗan bayanan shugaban kasa to ina ga Najeriya? Don haka waɗanda ke tunanen Amirka uwa ce ma bada mama to ba haka bane.

Domin duk abinda take yi bazarana ce kawai saboda barazana ce ma yasa take ƙoƙarin sai ta samu sanin halin da kowace kasa take ciki, domin kura ce ga tsaoro ga ban tsaoro".

Batun kwarmato da ma tonon sililin zargin leƙen asiri da Amirkan ke yi dai zai ci gaba da tada ƙura ba kawai saboda an sabawa ƙa'idar mutunci ta ƙasa da ƙasa ba, har ma da illar da hakan ke da ita ga harkokin tsaron kasashen duniya da dama.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Pinaɗo Abdu Waba