1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na tuhumar kamfanonin waje da siyan man sata

Yusuf BalaSeptember 20, 2016

Najeriya dai ta kasance kan gaba wajen fitar da albarkatun na man fetir a Afirka kafin Angola ta sha gabanta a watan Maris.

https://p.dw.com/p/1K5b9
Nigeria Port Harcourt Arbeiter auf Plattform Ölförderung
Fasa bututun man fetir a yankin Niger Delta ya sa Najeriya koma baya a fannin tattalin arzikiHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Najeriya na tuhumar manyan kamfanoni da ke hada-hadar albarkatun man fetir a kasar bisa zargin siyan man da ya haure Dala miliyan 12 ba tare da sanin mahukunta ba, sannan aka fita da shi zuwa Amirka tsakanin shekarun 2011 da 2014, kamar yadda mahukunta suka bayyana a ranar Talatan nan.

Babbar kotun shari'a da ke zamanta a Legas za ta fara sauraren shari'ar kamfanonin na Chevron da Shell da Eni da Total da Agip da Brasoil kamar yadda rijistar kotun ta bayyana.

Babu dai wani kamfani cikin wadanda ake tuhuma da ya mayar da martani kawowa yanzu. Najeriya dai ta kasance kan gaba wajen fitar da albarkatun na man fetir a Afirka har sai a watan Maris da Angola ta sha gabanta saboda aiyukan masu fasa bututun mai a yankin Niger Delta.