1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na kokarin cike gibin kasafin kudinta

Salissou BoukariFebruary 2, 2016

Gwamnatin Najeriya na tattaunawa da Babban Bankin raya kasashen Afirka da kuma Bankin Duniya domin samun rancen kudade na miliyan dubu biyu da miliyan dari biyu na dalar Amirka.

https://p.dw.com/p/1Ho57
Babbann bankin Najeriya

Tun farko dai hukumomin na Najeriya sun sanar cewa sai sun samo rancen kudaden da yawansu ya kai miliyan dubu 8,3 na dalar Amirka domin cika gibin kasafin kudin kasar. Najeriya da ke a matsayin wadda ta fi ko wace kasa a Afirka karfin tattalin arziki, ta gamu da rugujewar tattalin arzikinta tun bayan faduwar farashin danyan man fetir a kasuwannin duniya, ganin cewa dama kasar ta dawwama ne ga kudadan da take samu daga man fetir. Sannan ga batun sama da fadi da dumbun kudadan kasar da wasu 'yan kasar suka yi. Kasafin kudin na Najeriya dai na wannan shekara ta 2016, ya kai sama da Naira tiriliyan shida abun da ba a saba gani a kasar ba.