1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na fuskantar rudanin tattalin arziki

Salissou BoukariMay 26, 2016

Masana tattalin arziki a Tarayyar Najeriya sun yi amannar cewa kasar ta shiga cikin wani hali na rudanin tattalin arzikin wanda ba a ga irin sa ba shekaru 25 da suka gabata.

https://p.dw.com/p/1IumE
Nigeria Geld Geldscheine Naira in Lagos
Hoto: Getty Images

A wani abun da ke zaman alamu na kara lalacewar lamura ga batu na tattalin arzikin Tarrayar Najeriya, babban bankin kasar na CBN ya ce tattalin arzikin kasar na fuskantar barazana ta durkushewa a karon farko. Tun dai a cikin kusan shekaru 25 din da suka gabata, kasar ta Najeriya ba ta samu matsi da ma hali mawuyaci irin na tattalin arzikin da ya kai na shekarar da ake ciki ta 2016. A karon farko dai kasar na fuskantar asarar da ta kai kusan kaso hudu a cikin dari na tattalin arzikin kasar a farko na watanni uku na wannan shekara.