Najeriya: Mota ta hallaka yara 11 a Gombe | Labarai | DW | 21.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Mota ta hallaka yara 11 a Gombe

Kananan yara 11 ne suka mutu, yayin da wasu 17 kuma suka samu munanan raunuka a garin Malam Sidi da ke cikin jihar Gombe, sakamakon wata mota da ta kwace ta kuma fada tsakiyar jama'a.

Hadarin ya faru ne a dai dai lokacin da ake karatun Mauladin tunawa da ranar haihuwar Monzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a cewar hukumar 'yan sandan jihar. Katsewar birkin motar ne dai ya haddasa wannan hadari a cewar Ahmed Usman, daya daga cikin masu magana da yawun 'yan sandan, inda ya ce yaran sun kasance 'yan shekaru 11 zuwa 15  da haihuwa.

Wannan hadari dai ya harzuka jama'ar da ke wurin, inda nan take suka hau direban motar da duka, har sai da ya mutu. A kowace shekara dai, Musulmi a arewacin Najeriya, da ma duniya, na bikin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammed yardar Allah ta tabbata a gare shi na tsawon makonni, inda ake samun halartar dumbun jama'a.