Najeriya: ″Matsin tattalin arziki ya kawo karshe″ | Siyasa | DW | 05.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: "Matsin tattalin arziki ya kawo karshe"

Gwamnatin Najeriya ta ce tattalin arzikin kasar ya samu ci gaba na 0.55 cikin 100. To sai dai al'ummar kasa na masu bayyana cewa ba su kai ga gani a kasa ba.

Wannan muhimmin ci gaba da tattalin arzikin Najeriyar ya samu biyo bayan kawo karshe na koma-bayan da ya fuskanta tun daga 2016 da kasar ta amince da hakan ya nuna cewa, a rubu'i na biyu na wannan shekarar tattalin arzikin ya bunkasa fiye da yadda ya kasance a 2017, abin da ya nuna cewa bunkasar tattalin arzikin na shekara zuwa shekara ya kai sama da kashi 2.04 cikin 100 maimakon kashi 1.59 na 2016. Tattalin arzikin dai ya zabura ne bisa ci gaba a sassa guda hudu na harkar man fetir, aikin gona, masana'antu da kuma cinkaiyya.

Tattalin arzikin kasar ya samu wannan tagomashi ne bayan da ya kwashe rubu'i biyar yana ci gaba da tsukewa.

Ko mene ne muhimmancin wannan ga yadda ake kalon Najeriyar? Alhaji Sani Aminu Dutsinma, masanin tattalin arziki ne a Najeriya.

"Yana da tasiri sosai domin tasirinsa shi ne kamar yadda lokacin da aka ce tattalin arzikin Najeriya ya shiga hali na koma-baya mutane suka rinka dari-dari suna ja baya, haka nan lokacin da aka ce ya samu ci gaba, wadanda muke zawarcinsu za su shiga kasar don gudanar da harkokinsu."

Har yanzu al'umma na kokawa game da tsadar kaya a kasuwanni

Har yanzu al'umma na kokawa game da tsadar kaya a kasuwanni

Amma shin al'ummar Najeriya sun fara ganin wannan sauyi a rayuwarsu ta yau da kullum, ga ra'ayoyin wasu mazauna birnin Abuja.

"Mu dai har yanzu ba mu ga wani ci gaba ba daga kayan da muke saye, don in mun je kasuwa cewa suke farashi ya karu."

To amma in dai gwamnati ta ce an samu ci gaba me ke sanya ba'a kai ga ganin hakan ba a rayuwar al'ummar kasar? Malam El-Harun Muhammad masani ne a fannin ci gaban kasa da ke kwalejin kimiyya da fasaha da ke Kaduna.

"Samun kwanciyar hankali a yankin Niger Delta ya taimaka ainun ga halin da tattalin arzikin Najeriyar ke ciki, yayin da bunkasar aikin gona da darajar da abubuwan da ake nomawa suka taka kuma ke ci gaba da taka muhimiyyar rawa. Domin fannin aikin gona kadai ya samar da kasha 22.79 cikin 100 in aka kwatanta da kashi 21.43 na shekarar 2016."

Al'ummar kasar dai na cike da kyakkyawan fata na samun dorewar wannan ci gaba ga tattalin arzikin kasar da a yanzu kowa ke ji a jikinsa.

Sauti da bidiyo akan labarin