Najeriya: Matsalar samar da hasken wutar lantarki | BATUTUWA | DW | 27.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya: Matsalar samar da hasken wutar lantarki

Majalisar wakilai a Tarayyar Najeriya ta ce za ta binciki batun sayar da hannayen jarin kanfanin samar da hasken wutar lantarki na kasa, wanda ta ce sayar da shi bai yi wani tasiri ba.

Kama daga birnin Lagos cibiyar kasuwanci ta kasar ya zuwa Abuja da ke zaman fadar mulki dai,  matsalar rashin hasken wutar lantarki na zaman ruwan dare gama duniya a kasar. Al'amura dai na kara lalace wa a tsakanin kamfanonin da ke samar da hasken wutar ya zuwa ga masu raba ta dama dillallan iskar gas din da ke zama makamashi na wadatar da ita.

Ya zuwa karshen wannan mako dai yawan wutar kasar ya ragu zuwa kasa da Megawatt 3000, duk da sauyin hannu daga gwamnatin zuwa ga 'yan kasuwa, abun kuma da ya harzuka 'yan majalisar wakilan kasar da suka ce tura ta kai bango kuma hakuri na 'yan kasar ya kare. Sau dai-dai dai har kusan 16 ne Tarayyar Najeriyar ta fuskanci rushewar tsarin wutar a daukacin kasar a shekarar da ta shude, kuma tuni  kasar ta fara nuna alamar komawa ga wata rushewar farko a bana cikin tsakiyar wannan mako. To sai dai kuma jerin  matsaloli a fadar ministan samar da hasken wutar kasar Babatunde Fashola na zaman ummul aba'isin  lalacewar lamura.

Nigeria Babatunde Fashola (Getty Images/AFP/P. Utomi)

Babatunde Fashola ministan ayyuka da makamashi na Najeriya

"Akwai matsalar rashin kudi, ba a iya biyan masu samar da iskar gas, haka kuma ba a iya biyan su kansu kamfanonin samar da  hasken wutar lantarkin ba, ga kuma kwan gaba-kwan baya tsakanin masu samar da  ita da kamfanonin da ke rabonta, wadannan su ne batutuwan. Sannan kuma ga zagon kasa a sashen yamma na yankin Niger Delta, a yanzu da nake magana bututun Escravos zuwa Legas ba ya aiki, haka tashar daukar mai ta Forcados ba ta aiki, in kuma baka iya samar da mai ba to kuwa babu iskar gas."


Abun jira a gani dai na zaman sabo na bincike kan harkar da ake yi wa kallon kama da wasoso da dukiyar al'umma, a bangare na shugabannin da aka dora amana a hannunsu.

Sauti da bidiyo akan labarin