1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Martani kan dakatar da Babacir Lawal

Uwais Abubakar Idris
April 20, 2017

'Yan Najeriya na cigaba da tofa albarkacin bakinsu kan dakatarwar da aka yi wa sakataren gwamnatin kasar da shugaban hukumar leken asiri bisa aikata ba daidai ba.

https://p.dw.com/p/2bcty

Al'ummar Najeriya na cigaba da maida martani da ma sharhi kan da matakin da shugaban Najeriya ya dauka na dakatar da sakataren gwamnatin tarayya Babacir Lawal bisa zarginsa da cin hanci da kuma shugaban hukumar leken asirin kasar Ayodele Oke wanda ya ce wasu kudade da hukumar EFCC ta gano a boye a wani gida mallakin hukumarsa ne. Tuni dai shugaban na Najeriya ya ce ya kafa wani kwamiti karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa don gudanar da bincike kana ya  basu makonni biyu don gabatar da rahotonsu.