1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Majalisar dattawa ta nemi a sauke Babachir Lawal

Matakin da majalisar dattawan ta dauka na hukunta sakataren gwamnatin Najeriya tare da saukeshi daga mukaminsa bisa almubazzaranci da kudaden taimaka wa 'yan gudun hijirar rikicin Boko Haram ya sanya maida martani.

Majalisar dattawan Najeriyar ta nuna fushinta a kan abin da kwamitin bincike da ta kafa ya gano na bankado zarge-zargen aringizo da ma bada kwangiloli ga kamfanoni, don aikin tallafa wa mutanen da suka rasa muhallansu a sakamakon rikicin Boko Haram. Hasali ma dai an karbe kudadden ba tare da yin aikin ba, abin da ya sanya ta bukaci a hukunta sakataren gwamnatin tarayyar Najeriyar tare da yin murabus saboda shi ne shugaban shirin shugaban Najeriya a kan Arewa maso gabashin kasar.

Daukan wannan mataki wanda shi ne karon farko da aka yi wa wani babban jami'in gwamnatin Najeriya a karkashin shugaba Muhammadu Buhari dake yaki da duk wani batu na cin hanci da rashawa babban ala'amari ne a tarayyar ta Najeriya. DW ta yi kokarin jin ta bakin sakataren gwamnatin amma hakan ya ci tura.

Sai dai ga sakataren kwamitin da aka zarga Malam Umar Musa Gullani da ya yi wa kwamitin majalisar bayani a kan zarge-zarge ya yi shaida bayanin da ya yi wa kwamitin majalisar da a lokacin suka ce sun wankesu daga duk wani zargi. Ambaton suna kai tsaye da ma bukatar yin murabus a lamarin da yake mataki na zargi, cike yake da tambayoyi don rarrabe al'amura,

‘Yan Najeriya za su sa ido don ganin fitar da rahoto na biyu na bincike a kan wadanda ake zargin ci da gumin bayin Allah da  rikicin Boko Haram ya mayar da su ‘yan gudun hijira.

Sauti da bidiyo akan labarin