1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Majalisa ta yi watsi da Magu

A karo na biyu majalisar dattijan Najeriya ta ki yi watsi da nadin Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC da ke yaki da almundahana da kudaden jama'a a kasar.

Majalisa ta yi watsi da Magu

Majalisa ta yi watsi da Magu

Magu dai na zaman mai rikon mukamin shugaban hukumar ta EFCC. Wakilinmu na Abuja Abuja Uwais Abubakar idris ya ruwaito cewa majalisar dattijan ta ce ba za ta amince da shi ba, biyo bayan wani rahoto da ta ce ta samu daga hukumar tsaro ta farin kaya ta kasar wato SSS, wanda ya nunar da cewa ba shi da kimar da zai iya jagorantar hukumar ta EFCC, akwai cikakken rahoto a shirinmu na yamma.