Najeriya; Majalisa ta amince da kasafi na 2016 | Labarai | DW | 23.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya; Majalisa ta amince da kasafi na 2016

Yanzu dai 'yan majalisar wakilai da na dattawa a Najeriyar sun amince da wannan kasafi na 2016.

Nigeria Abuja Präsident Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari

'Yan majalisar dokoki a Najeriya sun amince da kasafin kudi da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar musu dan aiwatartwa a shekarar 2016, kasafin da ake gani ya zo da tsari da zai tallafa wa tattalin arzikin kasar ta Najeriya wanda a yanzu yake cikin rudani.

Yanzu dai 'yan majalisar wakilai da na dattawa a Najeriyar sun amince da wannan kasafi, abin da ya yi saura shi ne shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba masa hannu dan zama doka.Shugaba Buhari dai ya bayyana kashe kudi tsaba sama da triliyan shida wato kudin da suka kai Dala miliyan dubu 30 a watan Disamba abin da zai taimaka wajan samun bunkasa da samar da abbaben more rayuwa a kasar ta Najeriya.