1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta kaddamar da sabuwar ranar demokradiyya

June 7, 2018

Muhawara ta kaure tsakanin 'yan Najeriya kan matakin gwamnatin na canza ranar demokradiyya daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni da ta yi daidai da ranar da Janar Ibrahim Babangida ya soke zaben Abiola a 1993.

https://p.dw.com/p/2z6Tf
Regimegegner Nigeria Chief Moshood Abiola
Marigayi MKO AbiolaHoto: picture-alliance/dpa

Kasa da awoyi 24 da ayyana wata karramawar girma ga tsohon madugun gwagwarmayar zaben 12 ga watan Yuni na shekara ta 1993, ra’ayi ya banbanta cikin Tarrayar Najeriya a tsakanin masu tunanin an yi daidai da kuma masu danganta matakin da na neman cimma wata manufar siyasa. Kadan dai ya hana gwamnatin kasar ta kai ga ambaton MKO Abiolan a matsayin daya a cikin shugabannin Tarrayar Najeriya. Wata sanarwar fadar gwamnatin kasar ta ce Abujar tana shirin karrama Abiolan da lambar girma mafi daraja tare kuma da sauya ranar bikin demokaradiyya ta kasar ya zuwa ranar ta 12 ga watan Yuni tun daga shekarar da ke tafe.


To sai dai kuma sabon matakin na ci gaba da janyo muhawara ciki Tarrayar Najeriya a tsakanin masu tunanin an yi daidai da kuma masu kallon matsayin a idanu na siyasa. Wasu dai na kallon karrama jagoran gwagwarmayar na da ruwa da tsaki da sabuwar cacar bakin da ke tsakanin manyan sojoji na kasar, a yayin kuma da wasu ke masa kallon kokari na neman kuri’ar  mutanen Kudu maso yammacin kasar mai tasiri. Isa Tafida Mafindi dai na zaman jigo a cikin jam’iyyar APC kuma a fadarsa shugaban kasar ya yi daidai a cikin iskar da ke kadawa a kasar yanzu.

Nigeria Abuja - President Muhammadu Buhari und ehemaliger Präsident Olusegun Obasanjo
Shugaba Muhammadu Buhari da tsohon Shugaba Olusegun ObasanjoHoto: picture-alliance/NurPhoto/next24online

 

A ranar Talatar da ke tafe ne dai za ‘a yi bikin karramawa da ko baya na Abiolan za ta kuma kunshi Babagana Kingibe da ke zaman dan takarar mataimaki can baya, sannan kuma da Gani Fawehinmi da ya share lokaci cikin gwagwarmayar neman tabbatar da hallascin zaben.