1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kungiyar Miyetti Allah ta nuna damuwa

Salissou Boukari
January 14, 2018

A yayin da ake cece-kuce kan rikicin Fulani makiyaya da manoma da ya addabi wasu jihohin Najeriya, kungiyar Miyetti Allah ta yi kira game da ganin an hukunta masu laifi.

https://p.dw.com/p/2qpdm
Nigeria Boko Haram Anschlag Maiduguri
Hoto: Getty Images/AFP

Kungiyar Miyetti Allah ta Fulani Makiya a Najeriya, ta bukaci a hukunta duk wani wanda aka samu da hannu a kashe-kashen da suke faruwa da ake dangata 'ya'yan kungiyar tare da biyan diyya na asarar da ta faru ga mutanen da rikicin ya shafa a jihohin Benue da Taraba.

A taron manema labarai da kungiyar ta kira da marecen wannan Lahadi a birnin Abuja, kungiyar ta nisanta kanta da kokarin da ta ce ana yi na ba ta mata suna a matsayin kungiyar ‘yan tada a Najeriya.