Najeriya: Karuwar farashin kayayyakin bukatun yau da kullum | Siyasa | DW | 16.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Karuwar farashin kayayyakin bukatun yau da kullum

Hukumar kula da kididdigar al’amura ta Najeriya ta fitar da rahoton da ya nuna karuwar hauhawar farashin kayayyaki a cikin kasar a dai dai lokacin da al’ummar kasar ke kara shiga mawuyacin hali.

Nigeria Tomaten auf dem Markt in Port Harcourt (DW/M. Bello)

Kasuwar masu sayar da Tumati a Port Harcourt

Alkaluma na kididdiga da suka nuna karuwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriyar da ya karu daga kashi 18.3 zuwa kashi 18.48, ya kasance mafi yawa da aka samu tun daga watan Oktoba na shekarar 2005, inda ya fi shafar farashin kayan abinci da na bukatu na yau da kullum a dai dai lokacin da al'ummar kasar ke kara kokawa saboda koma bayan tattalin arziki.

Symbolbild Afrika Markt Bunt (P. U. Ekpei/AFP/Getty Images)

Mata da ke harkokin kasuwanci a Afirka

Karuwar farashin kayan ta zo kwanaki biyu bayan da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin shekara ta 2017 da ke cike da fatan shawo kan koma bayan tattalin arzikin kasar. A ‘yan watannin nan ne dai al'ummar Najeriyar sun kasance wadanda ke ci gaba da fuskantar yawaitar hauhawar farashin kayayyaki a kasar da ba haka aka saba ba a shekaru da dama da suka gabata. Najeriyar dai na cikin kasashen da ke fuskantar koma bayan tattalin arziki da sannu a hankali ke kara jefa rayuwar mafi yawan al'umma cikin ta ‘yan Rabbana ka wadatamu. Al'ummar kasar na sa ido cike da fatan samun sauyi na saukin rayuwa a shekara mai zuwa ta 2017 kamar yadda gwamnati ke alkawari duk da cewa da take yi ba fa laifinta ba ne wahalhalun da ake fuskanta.

 

Sauti da bidiyo akan labarin