1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

APC ta ce ba ta damu da ficewar Saraki ba

August 1, 2018

Gwamnatin Najeriya karkashin APC ta ce ko a jikinta game da sauyin sheka da Sanata Bukola Saraki ya yi. Dama fadar gwamnati na zarginsa da yi mata zagon kasa.

https://p.dw.com/p/32SnX
Nigeria Bukola Saraki
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Kasa da 'yan awoyi da sauyin sheka a bangaren shugaban majalisar dattawan tarrayar Najeriya Bukola Saraki, gwamnatin kasar ta ce ko a jikinta game da sauyin sheka ta Sarakin da fadar gwamnatin kasar ta zarga da yin zagon kasa ga harkoki na gwamnatin.

Duk da cewar an dade ana ta hasashe, amma aiyyana sauyin shekar a bangare na shugaban tarrayar Najeriya dai daga dukkan alamu ya girgiza daukacin fage na siyasar kasar ya zuwa yanzun.

Ko bayan kasancewarsa mafi girman iko da ya bar jam'iyyar APC mai mulki, ana kallon ficewar ta Saraki a matsayin wani yunkuri na karin karfi ga jam'iyyar PDP ta adawa da ta yi nisa a cikin karatun samo hanyar kwace mulki daga masu tsintsiyar da ke ci yanzu.

APC ta yi son barka da canja shekar Saraki

Ministan yada labaran Najeriya Alhaji Lai Mohammed
Ministan yada labaran Najeriya Alhaji Lai MohammedHoto: picture-alliance/dpa/K. Wigglesworth

To sai dai kuma ga fadar gwamnatin kasar ta Abuja fitar ta Saraki na zaman alheri a gareta kuma a fadar ministan yada labaran tarrayar Najeriyar Alhaji Lai Mohammed.

"In ka duba a shekaru uku da suka gabata a karkashin shugabancin Dr Bukola Saraki, majalisar dattawan Najeriya ta zama 'yar adawar da ko da hannun 'yan PDP take sai haka. Wannan gwamnatin ta wahala a hannu na majalisar da Saraki ke shugabanta. Ana jan kafa ga kasafin kudi, ana kaiwa akalla watan Yuni na kowace shekara kafin iya samun kasafi. Majalisar ta ki amincewa da nade-nade na shugaban kasar. A saboda haka gaba ta kai mu. Saboda a karon farko mun san ko su wane ne abokanmu na zahiri. Abin da muke da su da na zaman masu yi mana leke na asiri. Suna kiran su 'yan APC ne amma kuma suna wa jam'iyyar PDP aiki. Ga batun kujerarsa kuma wannan 'yan uwansa z asu yanke hukunci kanta."

Neman mafita

Tuni dai aka fara nuna alamun daukar mataki a kan hukuncin na Saraki tare da wata ganawa a tsakanin shugaban kasar da wasu zababbun 'yan majalisar dattawan game da shugaban jam'iyyar ta APC.

Jiya ba yau ba- Shugaba Buhari da Sanata Saraki lokacin da ake dasawa
Jiya ba yau ba- Shugaba Buhari da Sanata Saraki lokacin da ake dasawaHoto: DW/U. Musa

Ganawar kuma da ake jin kareta tare da tilasta sake bude majalisar da nufin kaiwa ga sauya shugabancin nata.

Ganawar kuma da a fadar Sanata Ali Ndume da ke zaman daya a cikin 'yan majalisar dattawa za ta basu damar yanke hukunci ga makoma ta Sarakin.

"Ba zai yiwu ba kana shugabancin gida, masu rinjaye ne suka zabe ka, amma ka bar shugabancin gidan, ka ce za ka ci gaba da rike wannan mukami. Kamata ya yi ya ba wa kanshi shawara ya ajiye shugabancin majalisar dattawan."

Ko bayan Sarakin dai shi ma gwamnansa na jihar Kwara ya bar jam'iyyar a yayin kuma da a Sakwato gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal shi ma ya yi adabo da jam'iyyar ta APC ya koma PDP.