Najeriya: IPOB kungiya ce ta ′yan ta′adda | Labarai | DW | 16.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: IPOB kungiya ce ta 'yan ta'adda

Gwamnatin Najeriya ta sanya kungiyar IPOB ta masu rajin kafa kasar Biafra a matsayin kungiyar 'yan ta'adda, inda cikin wata sanarwa ofishin ministan tsaron kasar ya ce kungiyar ta wuce gona da iri.

Nigeria pro-Donald-Trump-Kundgebung der Indigenous People of Biafra in Port Harcourt (Getty Images/AFP)

'Yan kungiyar IPOB suna zanga-zanga

Wannan dai ya biyo bayan binciken da jami'an tsaron Najeriya suka yi ne da kuma arangamar da ta wakana tsakanin sojojin kasar da 'yan kungiyar a yankin Kudu maso gabagashin kasar. An dai kafa kungiyar IPOB ta masu rajin kafa kasar Biafra a shekarar 2013, amma kuma sannu a hankali ta rikide ta koma wani babban kalubale na tsaro ga Tarayyar ta Najeriya a cewar John Enenche, mai magana da yawun  ofishin ministan tsaron kasar ta Najeriya.

Hukumomin tsaron sun kuma zargi 'yan kungiyar ta kafa kasar Biafra da laifin kai hare-hare ga wuraran da ke karkashin kulawar sojojin Najeriya dauke da makammai da suka hada da duwatsu, adduna, da kuma gurneti na man fetur, tare kuma da neman yin fito na fito da jami'an tsaron Najeriya. Sai dai kungiyar ta IPOB ta soki matakin wanda ta kira danniya da sojojin Najeriya ke nuna mata, inda ta ce sojojin sun kashe mutanenta da dama.