1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Harin sojoji bisa kukure a Zamfara

Uwais Abubakar Idris
October 27, 2017

A Najeriya kungiyoyin kare hakin jama’a sun maida martani kan sake samun hari bisa kukure da ake zargin sojojin Najeriya da kaiwa kan fararan hula a wani kauye da ke jihar Zamfara, zargin da sojojin suka musanta.

https://p.dw.com/p/2mcyj
China J-10 Militärjet
Hoton wani jiragin yaki na kasar ChinaHoto: Picture alliance/Photoshot/Y. Pan

Sake samun hari a kan fararan hula da sojojin Najeriya suka yi a kan wani matsugunin jama'a da ake kira Tungar kauyen Bagega a jihar Zamfara, ya harzuka  kungiyoyin kare hakin jama'a a kasar, inda suke bayyana bukatar daukan matakai na hakika da ma bincika al'amarin, musamman  yadda aka toshe duk wani labari na afkuwar lamarin fiye da kwana goma da faruwarsa. Kokarin kare rayukan fararen hula dai muhimin abu ne ga duk wani aiki na yaki da masu aikata miyagun laifuffuka.

Illegale Bergbau Aktivitäten in Bagega Zamfara Nigeria
Kauyen Bagega da ke cikin jihar Zamfara a NajeriyaHoto: Aminu Abdullahi Abubakar

"To abin takaici ne ganin yadda ake samun irin wannan hadaruka. Kuma ko da gayya ake yinsa ko kuma da da gayya ba, ya kyautu dai a yi bincike domin gano gaskiyar lamarin. Domin ya kasance ana azabtar da mutanen da ta kamata a bai wa kariya. Don haka dole ne a tashi tsaye na ganin wadanda suke da hannu cikin lamarin sun yi bayani."

Kakakin rundunar sojojin Najeryar Birgadiya Janar Sani Usman Kuka Sheka ya ce a bisa saninsu ana ta yada hotuna da ba na gaskiya ba ta shafukan sada zumunta, domin su basu da masaniya a kan afkuwar lamarin amma dai za su bincika.

"A hakikanin gaskiya yanzu da ake yayata shi a kafofin sada zumunta ba gaskiya bane ba ne, don na yi magana da brigade kwamanda ta daya ya ce mu sojojinmu bamu da labari, 'yan sanda ba su da labari suma jami'an tsaro na SSS ba su da labari, amma kokarinmu a kaucewa sake afkuwar wani kuskure don haka zamu bincika, amma in dai wannan ne to ba gaskiya ba ne."

Ko a tsari na yaki da masu kai hare-hare ana iya kaucewa afkuwar kukure irin wannan da ya kasance a karo na biyu da ake samun irinsa a Najeriyar. Sai dai abin tsoro shi ne hatsarin da irin wannan ka iya haifarwa ga yakin da sojoji ke yi a sassa daban-daban na Najeriyar. Yan zu dai za a sa idanu don ganin ko rundunar sojan za ta fitar da ba'asi a kan wannan batu kamar yadda ta yi alkwari.