1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Gobara ta kashe 'yan gudun hijira

Abdul-raheem Hassan
March 27, 2018

Gobara ta halaka mutane a sansanin 'yan gudun hijira a garin Rann mai tazarar kilomita 175 da birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno.

https://p.dw.com/p/2v3ot
Boko Haram Nigeria 14.2. Kwadon
Hoto: Getty Images/Aminu Abubakar

Rahotanni da ke fitowa daga Arewa maso gabashin Najeriya na cewa akalla mutane biyar sun mutu yayin da wata gobara ta barke a wani sansani makare da 'yan gudun hijira dubu 55.

Gobarar ta tashi ne sakamakon wutar da aka rura don dafa abinci a sansanin. Wutar ta dau akalla sa'oi uku ta na ci, ta kuma haddasa kone tantuna da sauran kayyaki da dama.

A yanzu dai tuni hukumomin ba da gaji da ke kula da yankin suka garzaya da wadan da suka jikkata daga gobarar. Garin na Rann da ke kan iyaka da Kamaru na da akalla mutane dubu 80 kuma jami'an agaji na Majalisar Dinkin Duniya sun sha fuskantar hare-haren mayakan Boko Haram.