1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya da Turkiya za su yaki ta'addanci

Yusuf BalaMarch 2, 2016

Shugaban na Najeriya mai masaukin baki Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin kasar za ta ci gaba da ayyukan da ta sa gaba duk da irin tangardar da ake samu.

https://p.dw.com/p/1I5ke
Türkei Erdogan
Shugaba ErdoganHoto: picture alliance/AA/E. Aydin

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa a shirye yake ya tallafawa kasar Najeriya a yakin da take yi da ayyukan ta'addanci wanda sakamakonsa kungiyar Boko Haram ta halaka dubban al'ummar kasar da suna fafutika ta kafa daular Islama.

Shugaban har ila yau ya kuma rattaba hannu kan yarjejeniya ta kasuwanci da tattalin arziki da mahukuntan na Najeriya, yarjejeniyar da shugaba Buhari ya ce somin tabi ne a harkar da ta shafi girka layukan bututun mai a harkokin kasuwancin albarkatun mai na kasar ta Najeriya.

Kafin dai zuwan shugaba Erdogan birnin na Abuja ya je kasar Ivory Coast da Ghana a ziyarar da ke zama ta kara kulla dangantaka ta kasuwanci da kasashen da ke zama mambobi a kungiyar kasuwanci ta kasashen Yammacin Afirka ko ECOWAS.

Shugaban na Najeriya mai masaukin baki Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin kasar za ta ci gaba da ayyukan da ta sa gaba duk da irin tangardar da a ke samu a tafiyar.

"Mun ki yarda mu samu sanyin gwiwa mun mai da hankali wajen samar da ci gaba a kasarmu, mu samar da aikin yi ga al'ummarmu mu samar musu da tsaro".